Uzairu badamasi

BARKA DA ZUWA SHAFI MAI ALBARKA

Alhamdulillah muna muku albishir insha Allah zamu dawo aiki gadan gadan!


Shafin farko

Haidar Ali

Hadisan Ma'asumai (AS)




قال الحسن العسكرى: إنَّ الوُصولَ إلَى اللهِ عَزَّوجَل َّسَفَرٌ لا يُدرَكُ إلّا بِامتِطاءِ اللَّيلِ

Imam Alhasan Al’askari (AS) ya ce: Hakika saduwa zuwa ga Allah tafiyace da baa riskar ta sai da tsayawa da dare.

قالت فاطمه الزهراعليها السّلام: مَن أصعَدَ إلَى اللهِ خالِصَ عِبادَتِه ِأهبَطَ اللهُ إلَيهِ أفضَلَ مَصلَحَتِه

FatimatuzZahra (AS) tana cewa: Duk wandaya kusanta da Allah yana maitsarkake ibadarsa Allah zai saukar masada mafificiyar maslaharsa (ya biya masa mafificiyarbukatarsa)

قال الامام الباقرعليه السّلام: حُبُّنا أهلَ البَيتِ نِظامُ الدّينِ .

Imam Al-Bakir(AS) ya ce: Sonmu Ahlil Baiti (AS) shi ne tsarin addini.

قال الامام على عليه السّلام: أصحابُ المَهديِّ شَبابٌ لا كُهولَ فيهِم إلّا مِثلُ كُحلِ العَينِ وَالمِلحِ فِيالزّادِ ، وأقَلُّ الزّادِ المِلحُ .

Imam Ali (AS) ya ce: Sahabban imam Mahadi (AS) samari ne, bamasu shekaru da yawa a cikinsusai kamar mashiyi da kuratandua guzurin matafiyi, ko kamar mafikarancin guzuri, gishiri.

قال الامام الصادق عليه السّلام: قالَ رسولُ اللهِ صلّى الله عليه و آله : ليسَ مِنّي مَنِ استَخَفَّ بِالصَّلاةِ ، لايَرِدُ عَلَيَّ الحَوضَ لا وَاللهِ .
Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Wanda ya wulakanta salla ba ya dagacikinmu, ba kuma zai zotafkina ba , a’a samWallahi!.

قال الامام الباقرعليه السّلام: أيُّما مُؤمِنٍ حافَظَ عَلَى الصَّلَوات ِالمَفروضَةِ فَصَلّاها لِوَقتِها فَلَيس َهذا مِنَ الغافِلينَ .

Imam Al-Bakir(AS) ya ce: Duk muminin da ya kiyayesalloli biyar na farillaya salla ce ta a lokutantawannan ba ya cikin gafalallu.

قال الامام الرضا عليه السّلام: بِرُّ الوالِدَينِ واجِبٌ وإن كانامُشرِكَينِ ولا طاعَةَ لَهُما في مَعصِيَةِالخالِقِ .

Imam Rida(AS) ya ce: Bin iyayewajibi ne ko da kuwamushirikai ne , amma baa biyayya a garesu a sabon mahalicci.



قال الامام على عليه السّلام: صِلُوا أرحامَكُم وإن قَطَعُوكُم

Imam Ali (AS) ya ce: Ku sadar da zumuncinkukoda sun yanke ku.

قال الامام على عليه السّلام : المُؤمِنُ نَفسُهُ مِنهُ في تَعَبٍوَالنّاسُ مِنهُ في راحَةٍ .

Imam Ali (AS) ya ce: Mumini ransa tana wahala dagagareshi amma mutane suna jindadi da nutsuwada shi.

قال الامام العسكرى عليه السّلام: ما تَشاوَرَ قَومٌ إلّا هُدوا إلى رُشدِهِم.

Imam Al-Hasan Askari (AS) ya ce: Matukar mutane suka yi shawarasai an shiryarda su zuwaga daidai.

قال الامام على عليه السّلام: صِيانَةُ المَرأَةِأنعَمُ لِحالِها وأدوَمُ لِجمالِها .

Imam Ali (AS) ya ce: Kamewar kan mace shi ya fi ye mata gahalinta ya fi kuma dauwamarda kyanta.

قال الامام على عليه السّلام: الصِّدقُ يُنجيكَ وإن خِفتَهُ ،الكَذِبُ يُرديكَ وإن أمِنتَهُ .

Imam Ali (AS) ya ce: Gaskiya tana tseratar da kaiko da ka ji tsoronta , karya tanahalakar da kai ko daka aminta da ita.

قال الامام على عليه السّلام: شَيئانِ لا يَعرِفُ فَضلَهُما إلّامَنفَقَدَهُما : الشَّبابُ ، وَالعافِيَةُ .

Imam Ali (AS) ya ce: Abubuwa biyu ba mai fahimtarkimarsu sai wanda ya rasasu :Samartaka , da Lafiya.

قال الامام على عليه السّلام: إنَّما الكَيِّسُ مَن إذا أساءَ استَغفَرَ وإذا أذنَبَ نَدِمَ .

Imam Ali (AS) ya ce: Kadai mai hankali shi ne wanda idan yayi mummuna zai nemi gafar , kumaidan ya yizunubi sai ya yi nadama.

قال الامام على عليه السّلام: لا يُسلَمُ لَكَ قَلبُكَ حَتّى تُحِبَّ لِلمُؤمِنينَ ما تُحِبُّ لِنَفسِكَ .

Imam Ali (AS) ya ce: Zuciyarka ba zata kubuta bahar sai ka so wa muminiabinda kake so wa kanka.



قال الامام الكاظم عليه السّلام: مَنِ اقتَصَدَ وقَنَعَ بَقِيَت عَلَيهِ النِّعمَةُ ، ومَن بَذَّرَ وأسرَفَ زالَت عَنهُ النِّعمَةُ .

Imam Al-Kazim(AS) ya ce: Wanda yayi tattali ya yi wadatarzuci ni’ima zata wanzu gareshi, amma wandaya yi barnaya yi almubazzarancini’ima zata gushe daga gareshi.

قال الامام على عليه السّلام: زَكاةُ الجَمالِ العَفافُ

Imam Ali (AS) ya ce: Zakkar kyau kamewa.

قال الامام على عليه السّلام: خَيرُ العُلومِ ما أصلَحَكَ .

Imam Ali (AS) ya ce: Mafificin ilimi wanda yagyara ka (ya shiryar da kai)

قال الامام على عليه السّلام: مَن كَثُرَ ضِحكُهُ ذَهَبَت هَيبَتُهُ .

Imam Ali (AS) ya ce: Wanda dariyarsa ta yawaitakwarjininsa zai tafi.

قال الامام على عليه السّلام: أحمَقُ النّاسِ مَن ظَنَّ أنَّهُ أعقَلُ النّاسِ .

Imam Ali (AS) ya ce: Mafi wautar mutane wandaya yi tsammaninshi ya fi mutane hankali.

قال الامام على عليه السّلام: عَجِبتُ لِلمُتَكَبِّرِ الَّذي كانَ بِالأَمسِ نُطفَةً ويَكونُ غَداً جيفَةً .

Imam Ali (AS) ya ce: Na yimamaki daga wanda yakegirman kai wanda jiya shi mani ne gobekuma zai zama mushe (matacce).

قال الامام على عليه السّلام: صاحِبُ السَّوءِ قِطعَةٌ مِنَ النّارِ .

Imam Ali (AS) ya ce: Mai mummunanaiki shi yanki ne na wuta.

قال الامام على عليه السّلام: ضادُّوا التَّوانِىَ بِالعَزمِ .

Imam Ali (AS) ya ce: Ku kishiyanci (ku yi maganin) sakaci(lalaci) da himma.

قال الامام على عليه السّلام: مَرارَةُ الدُّنيا حَلاوَةُ الآخِرَةِ

Imam Ali (AS) ya ce: Dacin duniya shi ne zakin lahira.


.
Copyright © 2018~2022.
( Uzairu Badamasi Sufi )
Harkarmusulunci@yahoo.com
All rights reserved

Bamu Da Alhakin Tallar Da Ake Sawa Akan Wannan Website Din


Disneyland 1972 Love the old s